A wannan zamanin samun kudi a yanar gizo (internet) na daya daga cikin hanya mafi sauki domin ta bayar da damarmaki da dama wanda mutum zai yi amfani dasu ya samu duk irin kudin da yake so ya samu batare da yasha wata wahala ba. A wannan rubutun zamuyi bayani dalla dalla akan yadda ake samun kudi ta hanyar bayyana ra’ayi akan wani abu a yanar gizo (internet). 

YADDA AKE SAMUN KUDI TA HANYAR AMSA TAMBAYA A INTANET  (SURVEY QUESTIONS)


A ko da yaushe kamfanunuwa suna bibiyar abokanan huldarsu ta kasuwanci domin suji ra’ayoyinsu ko kuma abun da suka fahimta dangane da huldarsu ta kasuwanci wanda ya shafi kayan da suke siyarwa (product) ko kuma aikin da suke yi ana biyansu (services), wannance tasa suke biyan makudan kudadi domin su samun wannan bayanan da suke nema. 


MANHAJOJIN DA AKE AMFANI DASU WAJEN BAYYANA RA’AYI DOMIN SAMUN KUDI 

Akwai manhajoji kala kala wadanda suke taimakwa kamfanunuwa wajen samowa bayanan dasuke buqata daga wajen mutane kokuma abokanan huldarsu ta kasuwanci, su wadannan manhajoji sune suke bayarda dama ga mutane suje su bayyana ra’ayinsu akan wani abu ko wani kamfani sukuma su biyasu a madadin wannan kamfanin. Mafi yawanci wadannan manhajoji suna da saukin mu’amala suna kawowa mutum tambayoyine dai dai da bayanan da ya saka musu a lokacin da ya fara yin amfani da manhajarsu. 


YANDA MUTUM ZAI ZABI MANHAJAR DA TA DACE DASHI 

Akwai mahajoji da dama wanda suke da mabanbantan tsari a yanar gizo wadanda suke aikin samar da tambayoyi (Survey question) da mutum zaije ya zaba ya amsa. Yana da kyau mutum ya lura sosai domin ya zabi manhajar da ta dace dashi sannan zata ke samar da wadatattun tambayoyi (survey question) wanda za ake samun kudi dasu akai akai batare da wani tangarda ba. Akwai hanyoyin da ake bi domin a zabi manhaja mafi mahimmancin cikinsu sune kamar haka. 

  1. Yanayin Biyan kudi: Yana kyau kafin mutum yayi rijista da manhaja ya lura da yanayin yanda ake biyan kudi a manhajar idan mutum amsa tambayoyin da ya kamata ya amsa, wasu manhajojin sunfi wasu biyan kudi mai yawa, domin samun biyan buqata dole ne mutu ya samu manhajar da take biyan kudi mai tsoka. 

  2. Wadatuwar Tambayoyin da za amsa: idan mutum zai zabi manhaja yayi qoqari ya samu manhajar da zata ke iya Samar da wadattun tambayoyin (Survey question)  da mutum zai ke zuwa yana amsawa a duk lokacin da yake da buqata domin sai mutum ya amsa tambbaya tukunnan zai samu kudi, idan manhajar da mutum ya zaba bata iya samar da tambayoyi akai akai zai kasance samun kudin mutum yayi qasa sosai. 

  3. Hanyoyin cire kudi: A lokacin da mutum zaiyi rijista da mnhaja domin samun kudi ta hanyar survey dole ne ya duba tsarin da manhajar take dashi na cire kudin da mutum ya tara a cikin manhajar, a nan mutum ya na da kyau ya zabi manhajar da take da hanyoyi kala kala da zai iya bi ya cire kudin da ya tara wannan zai bawa mutum dama ya cire kudinsa ta duk hanyar da yake so kuma take da suki kaman irin su paypal, payoneer, gift card da dai sauransu. 

  4. Dadin mu’amala: Idan mutum zai zabi manhaja ya duba manhajar da take da sukin mu’amala wacce zata taimaka masa yake amsa dukkanin tambayoyin da yake so ya amsa batare da wata tangarda ba. 


Ku danna link din dayake kasa domin samun bidiyo cikakke



DABARUN INGANTA SAMUN KUDI TA HANYAR AMSA TAMBAYOYI A YANAR GIZO  (SURVEY QUEASTIONS) 

Bayan mutum ya zabi manhajar da zai ke amsa tambayoyi (survey question) yana da kyau ya bi wadannan hanyoyin domin ya inganta samun kudinsa. 


  • Sanya cikakken bayani: Mutum yasa cikakken bayaninsa a manhajar da yake amfani da ita, wannan shine zai saka suke kawo masa tambayoyi akai akai wadanda suka dace da bayanen daya saka musu a wannan manhajar. 

Bayanai irinsu

  1. Suna 

  2. Sheakarar haihuwa 

  3. Fagen da mutum ya ke da kwarewa akai 

  4. Inda mutum yake zaune da dai sauransu 

  •  Mayar da hankali wajen amsa tambayoyi: Dole ne mutum ya mayar da hankali sosai wajen amsa dukkanin tambayoyin da aka kawo masa a manhajar da ya zaba domin su kamfanin da suka kawo wa mutum wannan tambayar (survey question) din suna da abun dasuke so su cimma sannan suna da yarjejeniyar da suka kulla da kamfaniN da suka basu wannan kwangilar, rashin yi musu aikinsu zai iya jawo musu matsala shine yasa a mafi yawan lokaci duk wanda baya mayar da hankali wajen yi musu aikinsu yanda ya kamata suna daina kawo masa tambayoyin kwatakwata wanda shi kuma zai rage masa samun kudi. 

  • Bibiya: Yana da kyau mutum yake bibiyar yanayin yanda yake gudanar da mu’amalarsa a duk manhajar da yayi rijiasta da ita domin yasan a matakin da yake da kuma matakin da yakamata ya dauka domin ya samu kudi mai yawa. 

  • Ya zabi manhaja mai kyau: Wajen zabar mahajar da mutum zaike amsa tambayoyi dole ne ya lura sosai domin wasu mahajojin sunfi wasu inganci, yana da kyau mutum ya duba mai dadi mu’amala, mai biyan kudi mai yawa, sannan mai saukin cire kudi idan ya gama amsa tambayoyin da ya kamata ya amsa.

  • Gayyatar mutane domin su zo suyi amfani da wannan manhajar abun da ake cewa referal:  wannan yana da mutikar tasiri wajen taimakawa domin yasamu kudi mai yawa domin mafi yawancin manhajoji suna da tsarin biyan wani kason kudi ta hanyar referals.

Ga wadansu zababbun manhajojin amsa tambayoyi (survey question) da ake samun kudi dasu sosai a yanar guzo.


Mutum zai iya bibiyarsu sannan ya karanta dukkanin bayanan yanda za a yi aiki dasu sannan ya zabi wanda ya dace da tsarinsa sai ya cike ya kuma fara samun kudinsa dashi. 


A KARSHE

Samun kudi ta hanyar amsa tambayoyi a yanar gizo damace da zata sa mutum ya mallaki kudi cikin qanqanin lokaci batare da shan wata wahala ba. Yana da kyau mutu ya zabi manhaja me kyau sannan ya mayar da hankali sosai wajen inganta samin kudinsa cikin kwanciyar hankali. Sai anjimanku!!